ILIMIN KASUWANCI A MATAKIN FARKO

Abubuwa 4 da ya Kamata a Fara Sani

(0 Rating)
₦2000
 Message Instructor

Highlights

  • Abubuwan da yin sana'a (entreprenuership) ya kunsa.
  • Halaye 8 na masu cin nasara a sana'a da kasuwanci
  • Abubuwan kusa da na nesa da ya kamata dan kasuwa ya sani
  • Ababen da ake lura da su wajen zabar sana'ar yi.
 Certificate

Yes

  Level

Beginner   

  Language

English (US)Course Details

Harafi daya ne ya bambanta nasara da asara a wajen rubutu, amma bambancin ma'anarsu da tasirinsu a rayuwarmu na da yawa sosai. Akwai sirri da rufin asiri a cikin sana’a, sai dai mutane na da tsoron yin sana’a domin gudun asara.

An shirya wannan bita domin bayani akan muhimman abubuawa guda 4 da mai son fara sana'a ko dan kasuwa ya kamata ya san su. Daga cikinsu akwai abubuwan da yin sana'a (entreprenuership) ya kunsa, da irin halayen masu cin nasara a sana’a. Akwai kuma ababen kusa da na nesa da mai sana'a ko dankasuwa ya kamata ya san su domin cin nasara, da kuma abubuwan da saninsu kan taimakawa mai son zabar sabuwar sana'ar da zai fara yi domin rage asara da da-na-sani.

A latsa Enroll Now a biya kudin yin wannan kwas, daga nan sai a yi rijista da shafin Braincert.com ta hanyar latsa Sign Up, da sanya cikakken suna da email, bayan yin rijista, a latsa Start Course domin fara koyon darussa.

Akwai takarkar shaidar yin wannan kwas ga wanda ya bi matakan yin wannan kwas ya kuma ci jarrabawa akan darussan da ya kunsa. Bayan gama darasi na karshe, sai ka latsa Start Test domin yin jarrabawa.

About Instructor

Penmark Academy

Cibiyar Dauwamammen Koyo ta Penmark (Penmark Academy for Lifelong Learning ) ce ta samar da wannan kwas. An kafa ta a shekara ta 2021 bayan an yi ma ta rijista da hukumar yi wa kamfanoni rijista watau, Corporate Affairs Commission. Cibiyar na gudanar da kwasa-kwasai akan darussan Turanci, Kasuwanci, Binciken Ilimi da sauransu. Sa’idu Sulaiman ne ya kafa cibiyar kuma shi ne Babban Darakta. Ya sami digirinsa na farko a fannonin Koyarwa da Tattalin Arziki tun 1985, sannan ya sami diploma da a ke yi bayan kammala digiri a fannin gudanarwa (watau Posgraduate Diploma in Management) a 1991. Ya kuma sami digirinsa na biyu a kan Gudanar da Kasuwanci. (watau Masters in Business Administration) a 1997, duk daga Jami’ar Bayero dake Kano.Ya koyar da Ilimin Tattalin Arziki a matakin ilimi mai zurfi, ya kuma wallafa littattafai a wannan fanni da sauran fannonin ilimi.

Course Review

click here